Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ghana ta gudanar da bikin aladun gargajiya na shekara
2019-08-05 09:58:06        cri

Bikin al'adun gargajiya na Asafotufiami na kasar Ghana, ya gudana cikin annashuwa, jiya Lahadi a garin Ada, wanda ke da nisan kilomita 70 daga gabashin birnin Accra.

A kan gudanar da bikin, wanda shi ne babban bikin gargajiya na kasar, a makon farko na watan Augustan kowacce shekara, domin tunawa da jarumtar magabata a yake-yaken da suka yi da makiya.

Jama'a da dama daga dukkan fannonin rayuwa ne suka yi tururuwa zuwa Ada, domin halartar bikin na gargajiya, inda mata da maza na iyalan gidan sarauta suka harba bindigar gargajiya cikin iska domin tunawa da jarumtar magabatansu da suka yi yaki tare da cin nasarar kan makiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China