Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ghana ta samu tallafin tura yara 90,000 zuwa makarantu
2019-07-13 17:08:02        cri
Wani jami'in kasar Ghana ya ce, wani shirin tallafi na kasa da kasa ya taimakawa gwamnatin kasar Ghana wajen kara adadin kananan yaran da ake sakawa a makarantun kasar.

Solomon Tesfamariam, daraktan shirin bada tallafin dake kasar Ghana ya bayyana a wani taron wuni guda na shirin taimakon al'umma na yammacin Afrika cewa, ta hanyar samun tallafin hukumomin kasa da kasa, shirin tallafawa kananan yara da yaki da wariyar jinsi na kasa da kasa reshen kasar ta Ghana, ya samu damar aiwatar da shirin shekaru biyar domin shigar da kananan yara masu rangwamen gata da wadanda suka rasa damar shiga makarantun a yankunansu.

Shirin shigarwa da koyar da yaran da basa makaranta na shekaru biyar ne, wato daga shekarar 2015 zuwa 2020, shirin ya kuduri aniyar shigar da kananan yara da basa makaranta kimanin dubu 90 daga wasu shiyyoyin kasar biyar.

Tesfamariam ya kara da cewa, "Shirin zai shigar da kananan yara maza da mata da suka fito daga wasu yankunan kasar inda zasu ci gajiyar shirin ta hanyar tallafa musu wajen samun ilmi a matakin farko, daga bisani za'a sauyawa kashi 70 bisa 100 na yaran zuwa matakin tsarin karatun firamare." (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China