Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rasha ta kira shirin Amurka na kare rijiyoyin man Syria a matsayin fashi
2019-11-12 11:14:56        cri
Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya kira shirin Amurka na barin dakarunta a Syria da nufin kare rijiyoyin man Syria daga 'yan ta'adda a matsayin fashi.

Yayin wani taron manema labarai da ya biyo bayan tattaunawarsa da takwaransa na Armenia, Zohrab Mnatsakanyan, Sergei Lavrov ya ce yunkurin na yi wa Syria fashi da karbe iko da rijiyoyinta na mai ya keta doka kuma ba zai haifar da wani alfanu ga Kasar ba, sai ma dai ya kara zaman dardar da barazana a wannan yanki na Syria.

Lavrov ya kara da cewa, suna jaddada cewa, sojojin Syria su mamaye dukkan yankunan kasar ba tare da bata lokaci ba. Yana mai cewa, wannan ne kadai zai kawo karshen ta'addanci da taimakawa wajen warware dukkan wasu batutuwa dake da alaka da warware rikicin siyasar kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China