Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Syria ya amince da yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin Rasha da Turkiyya kan yanayin arewacin kasarsa
2019-10-23 11:43:55        cri
Fadar Kremlin ta Shugaban kasar Rasha, ta ce shugaban Syria Bashar Al-Assad, ya goyi bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Shugaba Vladimir Putin da takwaransa na Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, biyo bayan tattaunawar da suka yi.

Vladimir Putin ya shaidawa Bashar al-Assad ta wayar tarho, tanade-tanaden yarjejeniyar da Rasha da Turkiyya suka cimma kan Syria, biyo bayan tattaunawar da ya yi da shugaba Erdogan.

Ya ce babban aikin shi ne dawo da cikakken 'yancin Syria da kuma kokarin ci gaba da hada hannu wajen samar da mafita ga yanayin da ake ciki a siyasance, ciki har da aiki karkashin kwamitin tsara kundin tsarin mulkin Syria.

A nasa bangaren, Shugaban na Syria ya godewa takwaransa na Rasha, inda ya bayyana cikakken goyon bayansa domin samun sakamakon aikin.

Masu tsaron iyakokin Syria sun shirya shiga kan iyakar Syria da Turkiyya tare da 'yan sandan sojoji na Rasha

Da farko, Rasha da Turkiyya sun cimma yarjejeniyar fahimtar juna tare da amincewa da tura dakarun hadin gwiwa yankunan da sojojin Turkiyya ke ayyukansu a Syria daga yau Laraba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China