Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da ba da tabbaci ga cinikayyar shige da fice
2019-07-11 13:39:11        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jagoranci taron majalisar gudanarwa ta kasar Sin a jiya Laraba, inda aka tabbatar da daukar karin matakan ba da tabbaci ga cinikayyar shige da fice, don habaka bude kofa, ta yadda za a samun bunkasuwa mai dorewa, da samar da karin guraben aikin yi.

Wadannan matakai dai sun shafi bangarori uku. Na farko, daidaita manufar kudi da ta buga haraji. Na biyu kuwa, kara ba da taimako ta fuskar hada-hadar kudi. Kuma na uku, himmatuwa wajen raya wasu sabbin sana'o'i, ciki hadda cinikayyar yanar gizo tsakanin kasa da kasa, da cinikayyar sarrafa kayayyaki, da gyaran kayayyaki a wurin da babu haraji da dai sauransu, da kuma kafa yankin ba da misali na cinikin shigo da kayayyaki. Kana na hudu, ingiza gudanar da ciniki cikin sauki, ta yadda za a samu ci gaba a fannin takaita ayyukan kwastam, da yin tsimin lokacin ratsa kwastam, da rage kudin da za a biya a kwastam.

Taron dai ya nuna cewa, rage kudin inshorar zamantakewa da kamfanoni za su biya, ya kasance wani muhimmin mataki ne na sassauta alhakin dake wuyansu, da ingiza da kuzarin kasuwa. Ya zuwa yanzu, inshorar zamantakewa iri daban-daban ta kasar Sin na tafiya yadda ya kamata, kuma hakan na da karfi biya cikin lokaci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China