Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta fadada cibiyoyin ciniki marasa shinge
2019-07-05 13:50:32        cri

Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta sanar a jiya Alhamis cewa za ta kafa sabbin cibiyoyin ciniki marasa shinge na gwaji wato (FTZs) guda shida, kana tana shirin fadada cibiyar ciniki marar shige ta Shanghai.

A wajen taron manema labarai da aka shirya, kakakin ma'aikatar kasuwancin Sin Gao Feng ya bayyana cewa, sabbin cibiyoyin da kuma aikin fadada cibiyar ciniki marar shinge ta Shanghai, zai kara baiwa kasar Sin damammakin bunkasa ciniki maras shinge da kuma samun damar inganta tsare tsaren kasar.

A karshen makon jiya ne, gwamantin Sin ta fitar da takardun jerin sassan da baki 'yan kasuwa ba za su iya zuba jari ba, daya na shafar yankunan cinikayya marasa shinge, dayan ma na shafar duk kasa baki daya, domin saukaka harkokin kasuwanci a fannin aikin gona, da ma'adinai, da ayyukan masana'antu, da kuma ayyukan bada hidima.

A kokarinta na kara bude kofa ga sauran fannoni, kasar Sin ta himmatu wajen kyautata ayyukan bada hidima da kuma samar da kyakkyawan muhallin zuba jari ga kasashen waje kana da kara yin musayar damammaki da sauran kasashe don su samu damar cin moriyar daga irin ci gaban da kasar Sin ta samu, inji Gao.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China