Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya tashi zuwa kasar Girka da Brazil
2019-11-10 16:25:18        cri
A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tashi daga birnin Beijing zuwa kasar girka, inda zai gudanar da ziyarar aiki, kafin kuma ya isa birnin Brasilia fadar mulkin kasar Brazil, domin halartar taro na 11 na shugabannin kasashe mambobin kungiyar BRICS.

Shugaba Xi ya samu goron gayyata ne daga shugaban kasar Girka Prokopis Pavlopoulos, da na Brazil Jair Messias Bolsonaro. Cikin tawagar shugaban na Sin akwai mai dakin sa Peng Liyuan, da kuma wasu jami'an gwamnatin kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China