![]() |
|
2019-11-10 15:38:26 cri |
A cikin wasikar ta sa, shugaba Xi ya ce, gina matakan aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya da Sin ta gabatar, na bukatar tabbaci ta fannin shari'a. Ya ce Sin a shirya take ta yi aiki da sauran kasashen duniya, wajen samar da managartan tsare tsaren shari'a, da kafa sahihan ka'idojin raya tattalin arziki da cinikayya bisa doron doka, masu dacewa kuma a bude.
Kaza lika Sin za ta nace ga aiwatar da matakan bunkasa ci gaban shawarar ziri daya da hanya daya, domin tabbatar da cin gajiya ga daukacin al'ummun kasashe daban daban.
Daga nan sai shugaba Xi ya bayyana fatan cewa, mahalarta taron zai su karfafa musayar ra'ayoyi, da cimma ra'ayi guda, wajen habaka tsarin shari'a, ta yadda hakan zai taimaka ga raya shawarar ziri daya da hanya daya.
Kungiyar ma'aikatan fannin shari'a ta kasar Sin ce dai ta dauki nauyin shirya taron, wanda ya samu mahalarta kusan 400 daga cikin kasar Sin, da kuma kasashen dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya 40, tare da wasu kungiyoyin kasa da kasa 4. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China