Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Namibia ta yi namijin kokari wajen kare hakkin yara
2019-06-17 09:35:36        cri
Shugaban kasar Namibia Hage Geingob, ya bayyana cewa kasarsa ta cimma manyan nasarori wajen kokarin kare 'yancin yara kanana da ba su tsaro, a yayin da kasar Namibiyan ta bi sahun kasashen Afrika don bikin tunawa da zagayowar ranar yaran Afrika.

Ana gudanar da ranar yaran Afrika wadda aka fara gudanarwa a karon farko a ranar 16 ga watan Yunin shekarar 1991. Taken bikin na bana shi ne "Aikin tallafin jinkan bil Adama a Afrika: Hakkin yara shi ne a sahun farko."

Geingob, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar raya yankin kudancin Afrika (SADC), ya karfafawa Namibia da shiyyar SADC baki daya gwiwa da su kara kokarinsu wajen tabbatar da samarwa yaran Afrika kyakkyawar makoma a nan gaba.

Geingob, da gwamnatinsa, suna kara sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukan da za su kara samarwa matasa da kananan yaran Afrika ingantacciyar rayuwa.

Sannan ya bukaci mambobi kasashen SADC su yi aiki tare da juna don tabbatar da kare 'yancin yaran Afrika karkashin shirin kula da marayu da yara marasa galihu da matasa na shiyyar SADC, da kuma hanyoyin da wasu shiyyoyin ke amfani da su wajen cimma wannan buri. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China