Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fannin kimiyya da fasaha na CIIE zai samar da makoma mai haske
2019-11-08 19:45:14        cri
A halin yanzu, ana fuskantar manyan sauye sauye a fannin kimiyya da fasaha da na masana'antu, kuma tattalin arzikin duniya na ci gaba da bunkasuwa, lamarin da ya sa ake ci gaba da zurfafa hadewar kimiyya da fasaha da tattalin arziki. Kana, bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na CIIE, ya kasance muhimmin dandali na yin gwaji kan hadewar kimiyya da fasaha da tattalin arziki. Yayin bikin baje kolin CIIE karo na farko, an kawo kayayyaki, da fasahohi na ci gaba a fannin kimiyya da fasaha sama da guda 100.

Bugu da kari, neman sabuntawa ta hanyar kimiyya da fasaha, ya kasance babban karfi na neman bunkasuwa, kana, sabbin fasahohi da sana'o'i da aka samar, bisa kwaskwarimar da aka yi a fannin kimiyya da fasaha, da masana'antu, za su kasance babban karfi na raya tattalin arzikin duniya. Kuma an kawo kayayyaki na zamani a fannin kimiyya da fasaha a bikin na CIIE, sabo da manyan kasuwannin da ake da su a nan kasar Sin.

Haka zalika, domin ra'ayoyin kariyar ciniki, da bin ra'ayin kashin kai da wasu kasashe suka nuna, ana bukatar sabbin hanyoyin raya tattalin arzikin duniya. Tabbas ne kayayyaki na ci gaba a fannin kimiyya da fasaha da aka nuna yayin bikin CIIE, za su samar da sabbin karfi wajen raya tattalin arzikin duniya. Don haka ya kamata a karfafa hadin gwiwarmu wajen neman sabuntawa, da yin mu'amala kan sakamakon da aka samu, tare da kuma karfafa aikin kare 'yancin mallakar fasaha, domin samar da wata makoma mai haske ga dukkanin bil Adama. Kuma tabbas ne "bikin baje kolin CIIE na kimiyya da fasaha" zai ba da gudummawa kan wannan aiki. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China