Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin baje kolin CIIE yana taimakawa kasashe masu tasowa wajen shiga dandalin kasa da kasa
2019-11-06 20:05:48        cri

A matsayin muhimmin dandali na hada hadar kayayyakin kasa da kasa, da kuma tallafawa kasa da kasa, bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE, ya samar da damammaki masu kyau ga kasashen duniya wajen neman ci gaba, musamman ma ga galibin kasashe masu tasowa. Bikin baje kolin CIIE ya samar musu wani dandalin yin gasa da kasashe masu karfin tattalin arziki cikin yanayin adalci.

Haka kuma, ana da kasuwa mafi girma a nan kasar Sin, bukatun al'ummar kasa yana kuma ci gaba da karuwa. Dandalin da bikin baje kolin CIIE ya kafa ya riga ya ba da taimako ga kasashe masu tasowa da dama wajen sayar da kayayyakinsu a kasuwar Sin.

Wadannan kasashe sun ji aniyar kasar Sin ta taimakawa kasashe masu tasowa, sun kuma cimma moriya sakamakon dunkulewar kasa da kasa. Lamarin da ya sa suka tabbatar da cewa, kasar Sin ita ce abokiyar arziki ga kasashe masu tasowa, wadda za su iya dogaro a kanta.

Kasar Sin mai bude kofa ga waje za ta inganta dunkulewar kasa da kasa, domin tallafawa karin kasashe maso tasowa da al'ummomi na kasashensu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China