Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Zambia zai yi amfani da bikin CIIE wajen kara shiga kasuwanni
2019-11-07 10:48:21        cri
Babban manajan kamfanin Moringa Wonder Plus na kasar Zambia Ernest Nyambe, daya daga cikin kamfanonin kasar dake halartar bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar Sin karo na biyu, dake gudana a birnin Shanghai na kasar Sin, ya bayyana cewa, zai yi amfani da bikin baje kolin na CIIE wajen kara shiga kasuwannin duniya.

Ernest ya bayyana cewa, bikin baje kolin CIIE yana da muhimmanci matuka, kana wata babbar dama ce da kowa ne kamfanin zai samu, kamar yadda nasa kamfanin zai yi amfani da wannan dama wajen tattara hajojinsa ga masu sayayya daga sassa daban-daban na duniya.

Ya ce, halartar bikin baje kolin, ya baiwa kamfanin damar kara shiga manyan kasuwanni na duniya

A don haka, kamfanin zai tabbatar da cewa, ya yi amfani da dukkan damammakin da ya samu a yayin bikin baje kolin. Ya ce, kasar Sin tana da babbar kasuwa, kuma a shirye kamfaninsa ya ke ya cimma wannan bukatu.

Shi dai Kamfanin Moringa Wonder Plus, ya shahara ne wajen samar da kayayyaki daga bishiyar Moringa, kana yana daya daga cikin kamfanonin da cibiyar cinikayya ta duniya ta dauki nauyinsu zuwa bikin baje kolin na CIIE.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China