Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Sin da ketare sun ba da shawarwarin raya ciniki a taron Hongqiao
2019-11-07 18:59:22        cri

A yayin taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin kasa da kasa na Hongqiao da aka yi a birnin Shanghai, masanan kasar Sin da na kasashen ketare kimanin dubu 4, sun ba da shawarwari game da kara dunkulewar kasa da kasa ta fuskar ciniki, da kuma kiyaye tsarin cinikin dake tsakanin kasa da kasa, inda suka fidda muryar "bude kofa ga waje da neman sabuntawa, da kuma yin hadin gwiwa domin cimma moriyar juna".

A matsayin muhimmin dandalin shawarwari kan harkokin kasuwanci, taron dandalin tattaunawar tattalin arziki na kasa da kasa na Hongqiao, ya mai da hankali kan batutuwa da dama da suka hada da yanayin gudanar da harkokin ciniki, da yin kwaskwarima ga kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, da kuma ciniki ta yanar gizo da dai sauransu, inda aka gayyaci muhimman masana guda 60 don su ba da jawabi a yayin taron, yayin da ake tattaunawa kan yadda za a kyautata tsarin tattalin arziki na duniya, domin raya tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.

A halin yanzu, ana gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, bikin da ba kawai dandali ne na hadin gwiwar kasuwanci da ciniki ba ne, har ma ya zama dandalin yin musayar labarai, da ra'ayoyi a tsakanin bangarorin da abun ya shafa.

A halin yanzu, akwai bukatar bude kofa ga waje da neman sabuntawa daga bangarori daban daban, tabbas dandalin zai ba da gudummawa wajen nuna adawa da ra'ayin kariyar ciniki da daukar matakai na kashin kai, tare da nuna goyon baya ga dunkulewar kasa da kasa kan harkokin tattalin arizki, ta yadda za a ba da taimako ga farfadowar tattalin arzikin duniya baki daya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China