Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tunisia ta halarci CIIE karo na biyu
2019-11-07 11:06:05        cri

Jami'ar kasuwanci ta ofishin jakadancin kasar Sin a Tunisiya Zhang Fengling ta ce, kasar Tunisiya ta nuna babbar sha'awa a bikin baje kolin kayayyakin da ake shigar da su kasar Sin karo na 2 (CIIE), fiye da wanda aka gudanar a karon farko a shekarar da ta gabata.

Zhang Fengling ta bayyana a zantawarta da Xinhua cewa, adadin mahalarta baje kolin daga Tunisiya ya karu daga mutane 5 zuwa 27, inda suka yi amfani da fili mai fadin sakwaya mita 136 don nune nune na kasar, da kuma sakwaya mita 108 wajen baje kolin kayayyakin masana'atun kasar a baje kolin na CIIE karo na 2.

Ministan ciniki ta kasar Tunisiya Omar Behi, shi ne ya jagoranci tawagar wakilan jami'an tattalin arziki da 'yan kasuwar kasar a baje kilon na CIIE.

Zhang Fengling ta bayyana cewa, kasar Tunisiya tana son tallata fannin yawon bude idonta da inganta yanayin muhallin zuba jari da kuma bunkasa cinikin kayayakin amfanin gona kamar man olive a bikin baje kilon kasa da kasar na kasar Sin.

Da take yabawa damar zurfafa hadin gwiwar ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da Tunisiya, ta ce kasarta a shirye take ta kara zurfafa hadin gwiwa da Tunisiya bisa tsarin daidaito da cin moriyar juna.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China