Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban sakataren kungiyar hadin gwiwar ciniki ta Masar ya amince da jawabin shugaba Xi Jinping
2019-11-08 14:17:37        cri
Bangaren masana'antu da cinikayya na kasar Masar sun sa lura sosai ga bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE karo na biyu, musamman ga jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping a gun bude bikin. Babban sakataren kungiyar hadin gwiwar ciniki ta kasar Masar Alaa Ezz ya amince da ra'ayin dunkulewar duniya gu daya da yaki da ra'ayin bada kariya ga cinikayya da aka bayyana a cikin jawabin shugaba Xi.

Malam Ezz ya furta fifikon kasar Masar da muhimmiyar rawa da kasar ke takawa wajen sa kaimi ga yunkurin dunkulewar tattalin arzikin yankin gu daya. Ya bayyana cewa, kasar Masar muhimmiyar kasa ce dake bin shawarar "ziri daya da hanya daya", kana hakan zai sa kaimi ga hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin, baya ga fadada ayyukan tattalin arziki da cinikayya zuwa yankin tekun Bahar Rum da yankin Afirka, a matsayinta na cibiyar cinikayya, matakin da zai amfanawa bangarori daban daban da abin ya shafa.

A ganin malam Ezz, a cikin jawabin shugaba Xi, matakan kara yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje na da babbar ma'ana ga bunkasuwar kasar Masar. Ya ce, kasar Masar ta dora muhimmanci sosai ga bikin CIIE, ganin cewa Sin na da babbar kasuwa, kana Masar na da fifiko a fannin amfanin gona, don haka yana fatan za a kara shigar da kayayyakin amfanin gona daga kasar Masar zuwa kasar Sin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China