Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe mutane 30 da ake zargin 'yan ta'adda ne a arewacin Burkina Faso
2019-10-09 10:41:12        cri
Dakarun gwamnatin Burkina Faso, sun kashe akalla mutane 30 da ake zargin 'yan ta'adda ne a Gorgadji dake arewacin yankin Sahelian na kasar.

Gidan talabijin na RTB na kasar, ya ruwaito cewa, sojoji da dama sun raunata yayin arangamar da aka yi a yankin arewacin kasar da ayyukan 'yan ta'adda suka daidaita.

Tun daga shekarar 2015 Burkina Faso ke fama da hare-haren ta'addanci, wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane sama da 500 da raba wasu sama da 280,000 da matsugunansu, ciki har da dalibai sama da 9,000. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China