Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane a kalla 20 sun mutu a sakamakon harin da aka kai wurin hakar ma'adinan zinari a kasar Burkina Faso
2019-10-06 17:00:37        cri
Wani jami'in hukumar kiyaye tsaron kasar Burkina Faso ya bayyana a ranar 5 ga wata cewa, an kai hari kan wani wurin hakar ma'adinan zinari dake jihar Soum ta arewacin kasar a ranar 4 ga wannan wata, wanda ya haddasa mutuwar mutane a kalla 20.

Jami'in ya ce, wasu dakaru ne suka kai hari kan wannan wuri ba zato ba tsamani a daren ranar 4 ga wannan wata, sun harbe mazaunan wurin dake aiki a kalla 20 har lahira. Ya zuwa yanzu, babu wata kungiya da ta sanar da daukar alhakin harin.

Tun daga shekarar 2015, an samu hare-hare sau da dama a kasar Burkina Faso, wadanda suka kawo illa ga halin tsaron kasar. A ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2018, wasu dakaru sun kai hari kan cibiyar sojojin kasar dake birnin Ouagadougou da ofishin jakadancin Faransa dake kasar Burkina Faso, wanda ya haddasa mutuwar sojoji 8. A ranar 9 ga watan Satumba na bana, an kai hare-hare biyu a jihar Sammatenga dake arewacin kasar, wadanda suka haddasa mutuwar mutane a kalla 29. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China