Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yi Allah wadai da tagwayen hare-haren da suka halaka mutane 29 a Burkina Faso
2019-09-10 21:11:17        cri
Shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat, ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan tagwayen hare-hare na baya-bayan da aka kaddamar kan jerin gwanon motoci dauke da abinci da wata babbar mota a yankin arewacin Burkina Faso mai fama da tashin hankali,hare-haren da suka halaka a kalla mutane 29.

Wata sanarwar da kungiyar ta fitar, ta bayyana cewa, hare-haren sun karara yadda ayyukan ke barazana a yankin sahel, da kuma bukatar gaggawa daga bangaren kasa da kasa na goyon bayan matakan da kasashen dake yankin ke dauka, musamman dakarun hadin gwiwar kasashen G5 Sahel, musamman Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da Jamhuriyar Nijar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China