Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bunkasuwar tattalin arzikin Sin na da makoma mai haske
2019-11-05 20:27:40        cri

Yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu a birnin Shanghai na kasar Sin. A yayin bikin, shugaba Xi ya ce, "tabbas, tattalin arzikin kasar Sin zai sami bunkasuwa, da kuma makoma mai haske".

Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya nuna muradun kasar Sin na ci gaba da raya tattalin arzikin kasar cikin yanayi mai kyau, kuma za ta ba da gudummawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

Ya ce kasar Sin za ta samar da Karin damammaki ga kasa da kasa a fannonin zuba jari, da karuwar tattalin arziki da dai sauransu, domin samun bunkasuwa cikin hadin gwiwa, da kuma ba da gudummawa wajen raya tattalin arzikin duniya cikin hadin gwiwa, da kuma karfafa dunkulewar kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China