Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi taron dandalin tattaunawar tattalin arziki na kasa da kasa karo na biyu a birnin Shanghai
2019-11-05 19:53:06        cri
A yau Talata ne aka bude taron dandalin tattaunawar tattalin arziki na kasa da kasa na Hongqiao, karo na biyu a birnin Shanghai na kasar Sin, kuma babban taken taron shi ne "bunkasuwar kasar Sin cikin shekaru 70 da suka gabata da dunkulewar bil Adama".

Wakilin ofishin siyasa, kana shugaban hukumar fadakar da jama'a na kwamitin kolin Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin Huang Kunming ya halarci bikin bude taron, inda ya kuma ba da jawabi mai taken "Yin mu'amala kan fasahohin neman ci gaba, Yin hadin gwiwa domin neman makoma mai haske".

Ofishin kula da harkokin labarai na gwamnatin kasar Sin ne ya gudanar da wannan taro, inda aka samu mahalartar masana da 'yan jaridu sama da dari 4, wadanda suka zo daga kasashe da yankuna sama da dari 1. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China