Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#CIIE#Xi: Sin za ta inganta hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa
2019-11-05 11:31:43        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana yau Talata a gun bikin bude taron CIIE karo na biyu cewar, kasar Sin mai jagorantar hadin kai tsakanin kasa da kasa ce, kuma mai mara bayan ra'ayin kasancewar bangarori daban daban ce, don haka za ta ci gaba da inganta hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban.

Haka kuma Xi ya furta cewa, Sin na da aniyar daddale yarjejeniyar cinikayya maras shinge mai babban mataki tare da dimbin kasashe, da ma himmatuwa wajen sa hannu cikin ayyukan hadin gwiwa tare da MDD, Rukunin kasashen G20, Kungiyar APEC, da ma kungiyar BRICS, a kokarin ciyar da yunkurin dunkulewar tattalin arzikin duniya gu daya zuwa gaba.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China