Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#CIIE#Sin za ta kara bude kasuwanninta ga baki masu zuba jari
2019-11-05 10:54:16        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana a yau Talata cewa, kasarsa za ta kara bude kasuwanninta ga baki masu sha'awar zuba jari da kara rage sassan da aka takaita musu zuba jari a baya.

Xi ya bayyana haka ne, a jawabin da ya gabatar yayin bude bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar Sin karo na biyu a birnin Shanghai. Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da inganta yanayin kasuwanci, ta yadda zai dace da kasuwa bisa doka da ma mataki na kasa da kasa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China