Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe 64 za su baje hajarsu yayin taron baje kolin CIIE na 2
2019-10-22 10:14:40        cri

Jimilar kasashe 64 da hukumomin kasa da kasa 3 ne suka tabbatar da za su halarci taro karo na 2, na baje kolin kayayyakin da ake shige da ficensu daga kasar Sin na kasa da kasa.

Yayin taron wanda zai mamaye fili mai fadin muraba'in mita dubu 30, kasashe za su baje irin ci gaban da suka samu a fannonin cinikayya da zuba jari.

Za a kafa rumfar kasar Sin a bana domin murnar cika shekaru 70 da kafa jamhuriyar Jama'ar kasar Sin da kuma nuna ci gaban da ta samu a fannin tattalin arziki da zamantakewa da kuma damarmakin da ake da su a sabon zamani.

Baje kolin karo na 2, zai gudana ne daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba a birnin Shanghai, inda daga baya kasar za ta tsawaita nata nune-nunen da karin kwanaki 8 da kuma bude shi ga jama'a inda za su biya kudin shiga, daga ranar 13 zuwa 20 ga watan Nuwamba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China