Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a kira taron dandalin tattalin arziki na kasa da kasa na Hongqiao karo na biyu
2019-10-24 20:24:03        cri
Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta bayyana cewa, taron dandalin tattalin arziki na Hangqiao karo na biyu da za a bude, mai taken " Bude kofa da kirkire-kirkire don alakar moriyar juna" zai hada da bikin bude taron da kuma wasu taruka biyar da za a shirya.

Za dai a gudanar da taron ne, a cibiyar taro da baje koli ta kasa dake birnin Shanghai, a ranar 5 ga watan Nuwamba, a lokacin da za a gudanar da bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su cikin kasar Sin karo na biyu.

Ana saran manyan baki sama da 60 da suka hada da 'yan siyasa daga wasu kasaahe da yankuna, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa, da shugabannin 'yan kasuwa na duniya da masana na kasar Sin da ketare ne za su halarci tarukan da za a shirya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China