Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CIIE karo na 2 ya ja hankalin kamfanoni sama da 250 daga cikin manyan kamfanoni 500 na duniya
2019-05-10 10:17:28        cri

Sama da kamfanoni 250 cikin manyan kamfanoni 500 na duniya da 'yan kasuwa ne za su halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na 2.

A cewar mataimakin daraktan hukumar kula da baje kolin, Sun Chenghai, za a fadada wurin gudanar da bikin zuwa murraba'in mita 300,000 daga 270,000 na bara, saboda karuwar masu bukatar halarta.

Sun Chenghai, ya ce za a baje karin fasahohin zamani yayin bikin, ciki har da fasahohin VR da AR da motoci mara matuki da sadarwar intanet tsakanin na'urori da dandalin hada-hadar kudi na Blockchain.

Jimilar kasashe da yankuna da hukumomin kasa da kasa 172 da kamfanoni sama da 3,600 ne suka halarci bikin na farko, wanda aka yi daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamban bara a birnin Shanghai, wanda ya kasance baje koli na farko na kayayyakin da ake shigar da su wata kasa da aka taba yi a duniya.

Yayin bikin, an cimma yarjeniyoyin cinikayyar kayayyaki da hidimomi na tsawon shekara guda da darajarsu ta kai dala biliyan 57.83.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China