Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gabatar da muhimmin jawabi a taron baje kolin CIIE karo na biyu
Mataimakin ministan cinikin kasar Sin Wang Bingnan, ya sanar a yau Talata cewa, kasar Sin ta shirya tsab don karbar bakuncin taron baje kolin kasa da kasa na kayyaykin da ake shigo kasar Sin daga kasashen ketare, wato (CIIE) a takaice karo na biyu, wanda za'a gudanar tsakanin 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba a birnin Shanghai.
Wang Bingnan, ya sanar da cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai gabatar da muhimmin jawabi a lokacin bikin bude taron baje kolin na (CIIE) karo na biyu.