2019-10-30 10:45:25 cri |
A cewar kididdigar baya bayan nan ta cibiyar dake sanya ido kan zuba jari ta kasa da kasa, baki dayan alkaluman FDI na duniya a watanni shidan farko na bana ya tasamma dala biliyan 640, inda ya karu da kashi 24%, ya zarta dala biliyan 517 na makamancin lokacin shekarar 2018, a daidai lokacin da tsarin sauye sauyen biyan harajin Amurka ya fara sanya wasu rukunin kamfanonin kasar Amurkar ke neman dawo da kudinsu gida.
Sai dai duk da takaddamar cinikayyar, har yanzu kasar Sin tana matsayi na biyu mafi karfin jarin na FDI a duniya. Amurka har yanzu ita ce ta farko mafi karfin jarin FDI wanda ya tasamma dala biliyan 143.
UNCTAD ta ce, hasashen da aka yi na shekarar nan baki daya yana nan bai sauya ba, kamar yadda aka yi hasashen tunda farko adadin zai karu zuwa kashi 5-10%. Sai dai kuma, koma bayan tattalin arzikin duniya da kuma yakin cinikin dake cigaba da faruwa zai iya zama babbar barazana ga karuwar tattalin arzikin na FDI. (Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China