Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkaluman OECD: Sin tana ci gaba da bude kofa ga kasashen waje
2019-10-31 10:51:49        cri

Kungiyar hada kai da raya tattalin arzikin kasa da kasa wato OECD ta gabatar da alkaluma, kuma mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya yi jawabi a Jiya Laraba cewa, wadannan alkaluma na shaida matakin da Sin take dauka na zurfafa bude kofa ga kasashen waje, kuma Sin za ta ci gaba da wannan manufa ba tare da kasala ba.

A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana, Geng ya ce, za a gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na 2 a birnin Shanghai nan da wasu kwanaki masu zuwa. Kasashe 63 za su halarci bikin nune-nune na kasa da kasa, kana kamfanoni sama da 3000 daga kasashe fiye da 150 za su halarci bikin nune-nune na kamfanoni. Abin lura shi ne, yawan kamfanonin Amurka da za su halarci bikin ya kai 192, adadin da ya zarce na sauran kasashe.

Geng yana mai cewa, wannan adadin ya nuna cewa, kamfanonin kasa da kasa ciki hadda Amurka sun amince da hasken makomar tattalin arzikin kasar Sin, da boyayen karfin kasuwar kasar, suna sa ran ci gaba da zuba jari a kasar har ma da zurfafa hadin kansu da kasar Sin.

Geng Shuang kuma ya yi kira ga kasashen duniya da su hada karfinsu wajen tinkarar manufar bangaranci da kariyar cinikayya, don samar da wani nagartaccen yanayi cikin daidaito da adalci, da kuma samar da damammaki masu kyau, ta yadda za a ingiza ciniki da zuba jari maras shinge da cikin sauki, da bunkasa tattalin arzikin duniya mai bude kofa cikin hadin kai. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China