Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin Sin na samun ci gaba matuka sakamakon bin tsari mai kyau
2019-09-24 15:46:02        cri

A cikin shekaru 70 da suka gabata bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, tattalin arzikin kasar ya samu babban ci gaba matuka. Alal misali, jimillar GDPn kasar Sin ta ninka sau 174 idan an kwatanta da ta shekarar 2018 da kuma 1952, wadda ta kai kaso 16% bisa na duniya baki daya. Ban da wannan kuma, adadin cinikayyar waje ya karu daga dala biliyan 1.13 a shekarar 1950 zuwa dala traliyan 4.6 a 2018, wanda ya ninka fiye da sau 4000.

Don haka ana iya ganin cewa, a cikin shekaru 70 da suka gabata, Sin ta canja daga kasar da ba ta da tushen tattalin arziki mai inganci da kimiyya da fasaha na zamani zuwa kasar da ke sahun gaba a duk duniya a fannonin masana'antu da cinikayyar kayayyaki da kudaden ajiyar musanya da ma jawo jarin waje. Bugu da kari kuma, Sin na himmatu wajen aiwatar da manufar kasancewar bangarori da dama, da gabatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" da ma hasashen "raya makomar bil Adama ta bai daya", a kokarin bayar da gudummawarta ga yadda ake tafiyar da harkokin duniya. Kuma dalilin da ya sa aka samu wadannan sakamakon shi ne sabo da Sin na da tsarinta mai kyau, kuma tana bin hanyar bunkasuwa da ta dace da halin da take ciki.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China