Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fara aikin kafa cibiyoyin gwajin bunkasa tattalin arzikin zamani da kirkire kirkire
2019-10-21 11:01:09        cri
Kasar Sin ta fara aikin kafa cibiyoyin gwaji guda 6 na ba da misali wajen bunkasa aikin kirkire-kirkire da ci gaban tattalin arziki na zamani bisa bayanai.

Za'a kafa cibiyoyin ne a sabon yankin Xiong'an dake lardin Hebei, da birnin Chongqing, sai kuma lardunan Zhejiang, Fujian, Guangdong da Sichuan, kamar yadda aka sanar a lokacin taron tattaunawar da aka gudanar a yayin taron karawa juna sani na kasa da kasa kan batun intanet dake gudana a garin Wuzhen dake lardin Zhejiang a gabashin kasar Sin.

Ana sa ran yankunan za su yi amfani da damammakin wajen zurfafa yin sauye-sauye da kuma zama zakaran gwajin dafi wajen bunkasa fannin tattalin arziki na zamani, a cewar Yang Xiaowei, mataimakin shugaban hukumar dake kula da yanar gizo ta kasar Sin.

An shirya kafa cibiyoyin gwajin ne da nufin zakulo wasu muhimman bangarorin dake shafar tattalin arziki na zamani, wanda ya hada da samar da sabbin hanyoyin kulla alaka, da samar da kudade, da nufin kaddamar da sabbin hanyoyin bunkasuwa, a cewar sanarwar da ka fitar dangane da shirin kafa cibiyoyin gwajin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China