Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: tsarin tashoshin caji masu matukar sauri ya kafu a tagwayen hanyoyi
2019-10-09 11:12:39        cri

Sakamakon kyautatuwar tashoshin caji a tagwayen hanyoyi a kasar Sin, motoci masu amfani da lantarki suna iya yin tafiya zuwa wurare masu nisa. A yau Laraba, Wakilinmu ya samu labari daga kamfanin kera motoci masu amfani da lantarki karkashin shugabancin kamfanin samar da lantarki na kasar Sin cewa, a cikin lokacin hutu na kwanaki 7 na murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin da ya gabata, motoci masu amfani da lantarki ne suka fi rinjaye a tagwayen hanyoyin kasar Sin, ta haka matsakaicin yawan lantarki da aka yi amfani da shi wajen caji a ko wace rana a wuraren caji na tagwayen hanyoyi, ya karu zuwa kilowatt-hour dubu 408, wanda ya ninka sau 3.6 bisa na zaman yau da kullum, kuma ya ninka sau daya bisa makamancin lokacin na shekarar bara.

A baya matsalar caji kan addabi masu tukin motoci masu amfani da lantarki. Don haka a shekarun baya-bayan nan, kasar Sin ta rubanya kokarin raya ababen caji da hada su a tagwayen hanyoyi. Ya zuwa yanzu, kamfanin samar da lantarki na kasar Sin shi kadai, ya kafa tashoshin caji masu matukar sauri 2080, inda ake da wuraren caji 8423 a tagwayen hanyoyi kusan kilomita dubu 50, wadanda suka hada birane 171 da ke cikin larduna 19 a kasar baki daya, balle ma sauran kamfanonin kasar. Matsakaicin nisan da ke tsakanin wadannan tashoshin caji bai kai kilomita 50 ba, kana cikin rabin awa kacal ake iya cajin mota. (Tasallah Yuan)  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China