Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Libya tana neman kwararrun Masar su yiwa sashen albarkatun manta garambawul
2019-10-28 11:40:31        cri
Shugaban kamfanin man fetur na kasar Libya (NOC), Mustafa Sanalla, ya sanar da cewa kasarsa tana neman yin hadin gwiwa da kamfanonin man kasar Masar domin gyara kayayyakin sashen albarkatun man kasar Libyan.

Sanalla ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da ministan albarkatun man kasar Masar, Tarek al-Molla, a birnin Alkahira.

Wata sanarwa da ma'akatar man kasar Masar ta fitar ta nuna cewa, jami'in kasar ta Libya ya bayyana aniyar kasarsa ta neman cin gajiya daga bangaren kwararrun kasar Masar wajen tsarawa da kuma aiwatar da shirin aikin gyaran bangaren albarkatun man kasar.

Al-Mulla ya jaddada aniyar kasar Masar wajen tallafawa yunkurin Libya na farfado da kamfanonin man fetur din kasar karkashin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

Ya bayyana cewa bangaren albarkatun man fetur na Masar a shirye yake ya gudanar da aikin garambawul a fannin albarkatun man na kasar Libya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China