Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Libya ta sanar da hallaka sojoji 16 na mayakan dake da sansani a gabashin kasar
2019-10-25 10:55:48        cri
Dakarun gwamnatin Libya mai samun goyon bayan MDD ta sanar cewa ta kashe sojojin dake da sansani a gabashin kasar kimanin 16 a kudancin birnin Tripoli.

Cikin wata sanarwa da gwamnatin mai goyom bayan MDD ta fitar ta bayyana cewa, dakarunta su ne ke cigaba da iko da sansanin Al-Yarmouk dake kudancin birnin Tripoli, bayan da suka yiwa mayakan Haftar dake da sansanin sojoji a gabashin kasar kofar rago, inda suka hallaka mayakan 16 kana suka kwace wasu tankokin yakinsu 3.

A daya bangaren kuma, sojojin masu sansani a gabashi sun ce, sun kaddamar da hare hare ta jiragen sama inda suka lalata wata ma'ajiyar makamai da kayan yakin sojoji a kudancin Tripoli.

Mayakan sojojin masu sansani a gabashi sun jima suna gudanar da atisayen soji tun a farkon watan Afrilu a yankunan babban birnin kasar Tripoli da nufin yakar gwamnati mai samun goyon bayan MDD, inda suke da yunkurin kwace ikon birni mafi girma a kasar da kuma kifar da gwamnatin mai samun goyon bayan MDD.

Dakarun sojojin masu sansani a gabashi, suna karkashin jagorancin Janar Khalifa Haftar, suna da dangantaka da gwamnatin dake da sansani a gabashin kasar, tun bayan da aka samu bambancin siyasa da rarrabuwar kawuna a kasar ta arewacin Afrika, lamarin da ya haifar da gwamnatin gabashi da kuma yammaci.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China