Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin ruwan Libya sun ceto bakin haure 300 a gabar ruwan yammacin kasar
2019-09-16 09:46:07        cri
Mai magana da yawun rundunar sojojin ruwan kasar Libya, Ayob Qassem, ya sanar a jiya Lahadi cewa, dakarunsu sun yi nasarar ceto bakin haure guda 300 a cikin wasu kwale-kwalen roba guda uku a gabar ruwan yammacin kasar.

Qassem ya shaidawa manema labarai cewa, bakin hauren da aka ceto, gailibi daga kasashen Afirka, mata ne da kananan yara, an kuma damka su a hannun sashen yaki da shige da fice ba bisa ka'ida ba, daga bisani kuma aka kai su cibiyar tsugunar da bakin haure.

Tun bayan boren shekarar 2011 da ya kai ga kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar marigayi Muammar Gaddafi, kasar Libya ta zama zangon da dubban bakin haure ke kokarin tsallaka tekun Meditareniya a kan hanyarsu ta shiga nahiyar Turai.

Yanzu haka, cibiyoyin tsugunar da bakin haure a Libya, sun cika makil da dubban bakin hauren da aka ceto ko kuma hukumomin tsaron Libya suka kama. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China