Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadaddiyar Daular Larabawa,Turkiya da kasashen yamma sun goyi bayan kamfanin man Libya
2019-09-23 09:06:30        cri
Kasashen Turkiya, da hadaddiyar daular Larabawa da Faransa da Jamus da Italiya da Burtaniya da kuma Amurka, a jiya Lahadi, sun bayyana goyon bayansa ga kamfanin samar da mai na gwamnatin kasar Libya (NOC) dake samun goyon bayan MDD.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da kasashen suka fitar, sun bayyana cewa, suna goyon bayan kamfanin mai na NOC a matsayin halastaccen kamfanin mai, mai zaman kansa na kasa, kana kamfanin man da ba shi da nasaba da wata jam'iyyar siyasa.

A 'yan kwanakin da suka gabata ne, kamfanin NOC, ya yi Allah wadai da yunkurin wasu mambobin majalisar gudanarwar kamfanin kasuwancin man fetur na Brega(BPMC) da sojojin dake gabashin kasar na raba kamfanin man fetur na Brega, daya daga rassan kamfanin

Gwamnatin Libya mai hedkwata a gabashin kasar, ta yi ikirarin cewa, kamfanin na NOC ya rage adadin man jiragen da yake samarwa a yankunan dake karkashin ikon sojojin dake gabashin kasar, don hana sojojin amfani da man a yakin da suke yi da gwamnatin dake samun goyon bayan MDD a ciki da kewayen Tripoli, babban birnin kasar.

Shugaban kamfanin NOC ya karyata zargin da ake yiwa kamfanin na rage yawan man jiragen da yake samarwa a yankunan gabashi da tsakiyar kasar, yana mai ikirarin cewa, man da kamfanin ke samarwa ya zarce bukatun fararen hula.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China