Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojin gabashin Libya ta kaddamar da gagarumin hari kan gwamnatin kasar a kudancin Tripoli
2019-09-22 16:31:28        cri
Kakakin rundunar sojin Libya dake da mazauni a gabashin kasar, Ahmad al-Mismari, ya ce rundunar ta kaddamar da gagarumin hari kan dakarun gwamnatin kasar da MDD ke marawa baya a kudancin Tripoli.

Ahmad al-Mismari, ya ce dakarunsu, sun kai hari kan dakarun na gwamnati ne a yankin Salah al-Din, da nufin kwace iko da shi.

A daya bangaren kuma, dakarun gwamnatin sun ce sun dakile yunkurin sojojin na yankin gabashi, shiga kudancin Tripoli.

Tun daga farkon watan Afrilu, rundunar sojin ta fara kaddamar da hare-hare da nufin kwace iko da Tripoli da kuma hambarar da gwamnatin da MDD ke marawa baya.

Ya zuwa yanzu, rikicin ya yi sanadin rayuka da jikkatar dubban mutane, tare kuma da raba kusan mutane 120,000 da matsugunansu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China