Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamntin Libya dake samun goyon bayan MDD ta yi tir da hare-haren da sojojin gabashin kasar ke kaiwa Tripoli
2019-09-28 17:03:59        cri
Gwamnatin Libya da MDD ke marawa baya, ta yi tir da hare-haren da sojoji 'yan adawa ke kai wa muhimman wurare a Tripoli, babban birnin kasar.

Cikin wata sanarwa, ta ce gwamnatin hadin kan kasar na yin tir da ci gaba da kai hare–hare kan muhimman wurare a Tripoli, yayin da jiragen saman yakin sojoji 'yan adawa na kasar, suka kai hari kan filin jirgin sama a kasa da kasa na Mitiga, da wasu muhimman gine-ginen gwamnati a tsakiyar birnin Tripoli, wanda kuma ya yi sanadin mutuwar fararen hula da lalata kadadorinsu.

Sanarwar ta ce, ci gaba da ayyukan na ta'addanci ya keta dokoki da yarjeniyoyin kasa da kasa kuma yana hargitsa birnin tare da kisa da razana fararen hula.

A ranar Alhamis ne rundunar sojin dake gabashin kasar ta sanar da kai hari kan filin jirgin saman na Mitiga dake Tripoli da lalata jiragen saman Turkiyya biyu, mallakin dakarun gwamnatin kasar.

Rundunar sojin karkashin Khalifa Haftar, ta yi ta kai hari filin jirgin sama na Mitiga, tana mai zargin gwamnatin kasar da MDD ke marawa baya, da amfani da shi domin ayyukanta na soji. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China