Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masar ta damu game da amfani da matakin soji wajen warware rikicin madatsar ruwan Nilu da ake zargin firaministan Habasha ya yi
2019-10-23 11:39:14        cri
Masar ta ce ta kadu tare da shiga damuwa game da jawabin da Firaministan Habasha, Abiy Ahmed ya yi, da ake zargin na magana kan amfani da matakin soji wajen warware rikicin madatsar ruwan Nilu.

Cikin wata sanarwa, ma'aikatar harkokin wajen Masar ta ce, bai dace Abiy Ahmed ya sanya batun matakin soji cikin abubuwan da za a iya amfani da wasu wajen warware rikicin kasarsa da Masar kan ginin katafariyar madatasar ruwan Habashar a kan kogin Nilu ba.

A ranar Talata ne kafafen yada labarai suka ruwaito shugaban na Habasha na cewa, "wasu na zancen amfani da karfi (wato Masar)". Yana mai cewa ya kamata a sani cewa, babu wani karfi da zai dakatar da Habasha daga gina madatsar ruwa.

Ya kara da cewa, idan akwai bukatar shiga yaki, to za su iya shiryawa. Idan wasu za su iya harba makami mai linzami, to wasu za su iya amfani da bama-bamai. Amma wannan ba shi ne ya dace da dukkan kasashen ba.

Ma'aikatar harkokin wajen Masar, ta ce Masar ta dade tana bayyana tattaunawa a matsayin hanyar warware rikicin dake da alaka da madatsar ruwan tsakanin kasahe 3 da suka hada da Masar da Habasha da Sudan. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China