2019-09-09 12:13:16 cri |
Manyan jami'an da suka halarci taron sun hada da Mohanmed El-Koosy, shugaban zartaswa na hukumar zirga-zirgar kumbuna ta kasar Masar, da Liao Liqiang, jakadan kasar Sin a kasar Masar.
Mista Mohanmed El-Koosy ya bayyana a wajen taron cewa, kasar Masar ita ce kasa ta farko da ta yi hadin gwiwa da kasar Sin a fannin fasahar tauraron dan Adam, karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya". Wannan aiki na nazari da kera tauraron dan Adam, a cewar El-Koosy, zai taka muhimmiyar rawa ga yunkurin kyautata yanayin hadin gwiwar kasashen 2 a wannan fanni.
A nasa bangare, jakadan kasar Sin a Masar Liao Liqiang ya ce, kasar Masar tana kan gaba a fannin zirga-zirgar kumbuna a nahiyar Afirka, kuma wannan aiki zai taimaka wajen daukaka matsayin kasar Masar a idanun al'ummun duniya, da karfafa zumuncin da ke tsakanin kasashen 2, da aza harsashi ga yunkurin raya wata al'umma mai makomar bai daya tsakanin bangarorin 2. (Bello Wang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China