Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe dan ta'adda 1 yayin wani bata kashi da 'yan sanda a Masar
2019-09-22 16:47:12        cri
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Masar, ta ce dan ta'adda 1 ya mutu, yayin da 'yan sanda 2 suka jikkata, yayin wani bata kashi da suka yi lokacin da 'yan sandan suka kai samame birnin Cairo, fadar mulkin kasar.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta ce dan ta'addan wanda dan kungiyar Hasm ne, ya kama wani gida a yankin Matariya na Cairo, a matsayin maboyarsa da kuma wajen adana makaman amfani da shi wajen aiwatar da ayyukansa.

Ta kara da cewa, 'yan sanda sun kai samame gidan, inda suka yi musayar wuta da shi, lamarin da ya kai ga mutuwarsa da jikkatar 'yan sanda 2.

'Yan sanda na daukar kungiyar Hasm a matsayin wani bangare na kungiyar 'yan uwa Muslimi ta Muslim Brotherhood da aka haramta.

Ayyukan ta'addanci a Masar, sun yi sanadin mutuwar daruruwan 'yan sanda da sojoji da fararen hula, tun bayan da sojoji suka hambarar da tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi a watan Yulin 2013, biyo bayan zanga-zanagr da aka yi na kin jinin mulkinsa na shekarar 1 da kuma kungiyarsa ta Muslim Brotherhood.

Wata kungiya mai mazauni a Sinai, da ta yi wa kungiyar IS mubaya'a, ta dauki alhakin galibin hare-haren ta'addanci da aka kai kasar a 'yan shekarun da suka gabata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China