![]() |
|
2019-09-17 09:22:44 cri |
Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta bayyana cewa, tattaunawar ta kwanaki biyu da ta gudana a birnin Alkahira, ta mayar da hankali ne kan matakan cikewa da tafiyar da aikin madatsar ruwan, ba ta kuma tabo yadda za a aiwatar da wadannan matakai ba.
Haka kuma taron bai tabo wani takamamman batutuwa ba, saboda yadda kasar Habasha ta ki tattauna shawarar da Masar ta gabatarwa tsakanin kasashen biyu.
A baya dai kasar Masar ta gabatarwa Habasha shawara kan tattaunawar da suka yi tun farko, da kuma yarjejeniya bisa manufa da shugabannin kasashen biyu suka sanyawa hannu a watan Maris na shekarar 2015, wadda ta bayyana cewa, bangarorin uku sun amince kan dokokin cikewa da gudanar da madatsar ruwan. (Ibrahim Yaya)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China