Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An hallaka 'yan ta'adda 15 a wani samame da 'yan sanda suka yi a Sinai na Masar
2019-09-30 11:22:12        cri
Wata sanarwa da ofishin ministan cikin gidan kasar Masar ya fitar, ta ce rundunar 'yan sandan kasar ta hallaka akalla 'yan ta'adda 15, yayin wani samame da suka kaddamar a birnin Arish dake lardin Sinai a arewa maso gabashin kasar.

Rahotanni sun nuna cewa, samamen ya biyo bayan wani bincike da aka gudanar, game da ayyukan wani gungun 'yan ta'adda dake samun mafaka a wata gona dake Arish, inda suke shirya dabarun kaddamar da hari kan gwamnatin kasar, lamarin da ya kai ga yiwa gonar tsinke, aka kuma yi musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan ta'addan.

Baya ga 'yan ta'addan 15 da suka rasu, 'yan sanda sun kuma gano manyan bindigogi 9, da wasu kanana 3, da ababen fashewa 2, da ma wasu damara mai dauke da ababen fashewa a cikin kayan bata garin.

Wannan dai lamari na zuwa ne 'yan kwanaki, bayan da rundunar sojojin kasar, tare da hadin gwiwar 'yan sanda, suka bayyana kisan wasu 'yan ta'adda su 118, a yankin na Sinai. To sai dai kuma an ce akwai jimillar dakarun soji 10, da wasu suka rasu wasu kuma suka jikkata, yayin bata kashin.

Kasar Masar dai na fama da ayyukan masu tada kayar baya, wadanda suka hallaka daruruwan 'yan sanda, da sojoji da ma fararen hula, tun bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Mohamed Morsi a watan Yulin shekarar 2013, sakamakon wata gagarumar zanga zangar kin jinin gwamnatinsa da ta barke a kasar, inda daga bisani gwamnatin kasar mai ci ta haramta ayyukan kungiyar "Muslim Brotherhood" ta tsohon shugaba Morsi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China