Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar UNHCR ta jinjinawa matakin da nahiyar Afrika ta dauka na kwashe 'yan gudun hijira daga Libya
2019-09-14 16:34:59        cri
Babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD Filippo Grandi, ya yi maraba da yarjejeniyar da aka cimma a wannan makon, tsakanin Tarayyar Afrika AU da kasar Rwanda, inda za a kafa wurin yada zango ga 'yan gudun hijira da aka kwaso daga kasar Libya

Cikin wata sanarwa, Fillipo Grandi, ya bukaci sauran kasashe su yi koyi da irin wannan hobbasa ta hanyar daukar matakan ceton rayuka.

Karkashin yarjejeniyar, Rwanda za ta karba tare da bada kariya ga 'yan gudun hijira da masu neman mafaka da aka kwaso daga Libya. Inda ake sa ran rukuni na farko na mutum 500, zai kunshi yara da matasa dake cikin hadari.

Kwamishinan ya ce ana tsananin bukatar sauran kasashe su yunkura su ma, don taimakawa wajen fitar da mutane daga hadari da kuma samar da mafita.

A cewar MDD Sama da 'yan gudun hijira 3,600 da masu neman mafaka ne yanzu haka ke tsare a cibiyoyin da ake tsugunar da su a Libya, inda galibinsu ke fuskantar cin zarafi mai tsanani da kasancewa cikin hadarin rikicin dake wakana a kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China