Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu fama da kangin talauci ya ragu da miliyan 150 a yankunan karkarar kasar Sin cikin shekaru 8 da suka gabata
2019-09-24 19:56:29        cri
Bisa "rahoto game da yadda ake fama da talauci a Asiya" da aka fitar a yau Talata, an bayyana cewa, bayan da gwamnatin kasar Sin ta dauki kwararan matakan fama da kangin talauci a duk fadin kasar a shekarar 2013, yawan masu fama da kangin talauci, da yawan wadanda suke kan fama da halin talauci a yankunan karkarar kasar, dukkansu sun ragu sosai.

Rahoton ya nuna cewa, yawan masu fama da talauci ya ragu daga miliyan 165.67 a shekarar 2010 zuwa miliyan 16.6 a shekarar 2018, wato ya ragu da kimanin miliyan 150.

Kaza lika yawan wadanda suke cikin halin fama da talauci ya ragu daga kashi 17.2 cikin dari a shekarar 2010 zuwa kashi 1.7 cikin dari a shekarar 2018.

Dandalin tattaunawar batutuwan Asiya na Boao ne ya fitar da wannan "rahoto game da yadda ake fama da talauci a Asiya".

Bisa shirin da gwamnatin kasar Sin ta tsara, kasar Sin za ta cimma burinta na kafa wata al'umma mai matsakaicin karfi a shekarar 2020, wato, za ta zama kasa mai tasowa ta farko wadda za ta ci nasarar kawar da kangin talauci a duk fadin kasar. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China