Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kawar talauci a dukkan yankunan kasa
2019-10-15 10:28:02        cri

Darektan ofishin kula da aikin yaki da talauci na majalisar gudanarwar kasar Sin Liu Yongfu ya bayyana a baya-bayan nan cewa, ya zuwa karshen shekarar 2019, kashi 95 bisa dari na matalauta za su cimma nasarar fita daga kangin talauci, kana, kashi 90 bisa dari na garuruwa masu fama da talauci za su fita daga cikin jerin garuruwa matalauta.

A shekarar 2019, ake cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyyar jama'ar kasar Sin. Kuma cikin wadannan shekaru 70 da suka gabata, mutanen kasar suna ci gaba da dukufa wajen kawar da talauci bisa jagorancin da gwamnatin kasar ta yi musu, inda har suka nemi wata hanyar kawar da talauci da ta dace da halin musamman na kasar Sin. Lamarin da ya sa, mutanen kauyuka masu fama da talauci sama da miliyan dari 7 suka cimma nasarar kawar da talauci. Kuma kasar Sin ta kasance kasar da ta fi samun raguwar masu fama da talauci, kana ita ce ke kan gaba wajen cimma muradun samun bunkasuwa na MDD. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China