Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta cimma nasarar rage talauci shekaru 10 kafin lokacin da aka tsara
2019-09-24 19:54:49        cri

Yau Talata ne a nan Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce a shekarar 2020 ne kasar Sin za ta cimma nasarar rage talauci, shekaru 10 kafin lokacin da aka tsara, wato za ta fitar da dukkan mazauna yankunan karkara daga kangin talauci. Wannan ita ce gudummawa mafi girma da kasar Sin za ta bayar wajen aiwatar da ajandar ayyukan samun ci gaba mai dorewa a shekarar 2030 a duniya.

Ban da haka kuma, har kullum kasar Sin na himmantuwa wajen yin hadin gwiwa da kasa da kasa wajen raya kasa.

A yammacin ranar 24 ga wata bisa agogon wurin, MDD za ta bude taron kolin manufar samun ci gaba mai dorewa a hedkwatarta a birnin New York, inda za a waiwayi yadda aka aiwatar da ajandar a duniya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China