Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci EU ta mutunta dangantakar da ke tsakaninsu, ta kaucewa tsoma baki kan batun HK
2019-08-18 15:57:55        cri

Babban wakilin Tarayyar Turai kan harkokin kasashen waje da manufofin tsaro, ya fitar da wata sanarwa dake bayyana damuwar Tarayyar game da yanayin da ake ciki a yankin HK, lamarin da ya harzuka kasar Sin.

Kakakin Tawagar Sin a EU, ya yi tsokaci kan sanarwar, inda ya jadadda cewa, harkokin HK, harkoki ne na cikin gidan kasar Sin, wadanda ba sa bukatar shigar wata gwamnatin waje ko kungiya.

Kakakin ya ce, bangaren EU, ya yi biris da adawar da kasar Sin ta nuna, yana ta ci gaba da tsoma baki cikin batutuwan HK da harkokin cikin gidan kasar.

Ya ce wannan yunkuri ya damu kasar Sin, kuma tana matukar adawa da shi.

Ya kara da cewa, tun bayan dawowar HK babban yankin kasar Sin, da manufar kasa daya mai tsarin mulki 2, al'ummar HK ke jan ragamar yankin, kana an sakar musu mara suna cin gashin kai yadda ya kamata.

Har ila yau, ya ce al'ummar Hong Kong sun mori 'yanci da hakkokin da a baya ba su samu ba.

Kakakin ya ce Kasar Sin ta na bukatar EU, ta kiyaye dokokin kasa da kasa da ka'idojin dangantakar kasa da kasa, domin kada ta illata kyakkyawar alakar dake tsakaninsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China