Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar Sin ta yi watsi da kalaman EU kan yankin Hong Kong
2019-08-15 10:44:28        cri
Kakakin tawagar kasar Sin dake kungiyar tarayyar Turai (EU), ya sanar a jiya Laraba cewa, kasarsa ta yi Allah wadai da sanarwar da kungiyar tarayyar Turai ta fitar mai cike da rudarwa da karya kan yankin musamman na Hong Kong.

A ranar Talata ne dai, sashen kula da harkokin kasashen waje na kungiyar EU, ya fitar da wata sanarwa game da halin da ake ciki a yankin na Hong Kong, inda ya yi kira ga dukkan sassa da su kai zuciya nesa su kuma guji aikata duk wani nau'in tashin hankali. Sanarwar ta kuma bayyana muhimmancin amfani da matakai na siyasa da tattaunawa daga dukkan fannoni.

Kakakin ya bayyana cewa, Hong Kong, wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba, kuma harkokin cikin gidan yankin, batu ne na harkokin cikin gidan kasar Sin. Yana mai cewa, bangaren EU, ya sake furta kalaman da ba su dace ba game da yankin Hong Kong, ba tare da amincewar kasar Sin ba.

Ya yi nuni da cewa, abin da ya faru a yankin, yanzu yana kokarin rikidewa zuwa mummunan tashin hankali, kuma duk wani kokari da 'yan sandan yankin ke yi na amfani da matakan da doka ta tanada kan tsageru masu karya doka, ana canja masa ma'ana kuma ba gaskiya ba ne, lamarin da kasar Sin ta yi Allah wadai da shi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China