Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana adawa da kalaman da OHCHR ya furta game da Hong Kong
2019-08-15 11:04:26        cri
Tawagar kasar Sin dake ofishin MDD a Geneva, ta bayyana a ranar Talata cewa, mai magana da yawun ofishin babban kwamishinan kare hakkin bil-Adam na MDD dake Geneva, ya furta wasu kalaman da ba su dace ba game da yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.

A sanarwar da ya fitar, kakakin tawagar kasar Sin, ya bayyana cewa, kalaman ofishin na MDD, tsoma baki ne a harkokin cikin gidan yankin Hong Kong, kuma batu ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar Sin, ya kuma aike da mummunan sako ga tsagerun dake boren da ya saba doka.

Don haka, tawagar kasar Sin ke cewa, kasarta ta bayyana rashin jin dadinta matuka da ma yin Allah wadai da kalaman.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China