Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Birtaniya ya bayyana matsayin gwamnatin Sin kan Hong Kong
2019-07-04 16:26:27        cri
Jakadan Sin dake Birtaniya Liu Xiaoming ya kira taron manema labarai a jiya Laraba, inda ya bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin kan batun kutsa kai cikin ginin majalisar dokokin Hong Kong da wasu masu tsattsauran ra'ayi suka yi a kwanakin baya, inda ya nuna matukar rashin jin dadi gami da adawa da shisshigin da Birtaniya ta yi cikin harkokin yankin Hong Kong da na kasar Sin.

Jakada Liu ya ce, Hong Kong wani yankin musamman ne na kasar Sin, Hong Kong ba a karkashin mulkin mallakar Birtaniya ya ke ba. Ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin na yin tsayin daka wajen kare 'yanci da tsaro da muradun bunkasuwarta, kana tana adawa da duk wani katsalandan da kasashen waje suka yi a harkokin cikin gidanta.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China